ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Masu ilmin harshen Hausa a Najeriya sun kai miliyan ɗari da ashirin

An yi wannan bayani a wani taro wanda aka yi game da yaɗuwan harshen Hausa.

___5964630___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___5964630___2016___12___29___8___hausa-people

An yi rahoto cêwa masu ilmin harshen Hausa sun kai yawan miliyan ɗari da ashirin. An saki wannnan rahoto a wani taro wanda aka yi a Jamiʼar Ahmadu Bello, cikin Birnin Zaria, a Jihar Kaduna. Malamin Sashin Harsuna da Alʼadun Mutanen Afrikiya suka shirya wannan taro.

A cikin wannan rahoto wanda ʼƴan jaridan Hukumar Labarai na Najeriya (NAN) sun ƙarba daga hannun Likita Balarabe Ɗanladi, an yi bayani cêwa yawan mutane yana cikin fihirisa na zaɓin harshe wanda za a tallafa domin amfanin da a matsayin harshen tarayyar alʼumma.

"Wannan shi ne domin harshen Hausa yana da masu amfani da shi a kowane wuri cikin duniya. Akwai rukuni biyu na harshen hausa. Akwai ʼƴan kasa (asalinsu ƙasar Hausa) da kuma wanɗanda sun koyi ilmin harshen Hausa."

"A ƙasar Najeriya, ʼƴan ƙasar Hausa sun wuce yawan miliyan sabaʼin. Waɗanda suka koyi harshen Hausa sun kai yawan milyan arbaʼin zuwa hamsin."

ADVERTISEMENT

Wannan rahoto ya bayyana cêwa masu ilmin harshen Hausa sun kai kashi ɗaya daga cikin ukku na yawan mutanen Najeriya. An bayyana cêwa masu amfani da harshen Hausa suna da yawa cikin Najeriya da ƙasashen waje. "Saboda haka, ya kamata harshen Hausa ya zama harshen tarrayar alʼumma, na yin hulɗa da harkoki a Najeriya."

"Wannan nazari shi ne baratar da zai sa gwamnati su inganta da kuma karfafa harshen hausa a Najeriya gaba ɗaya."

" Wannan muhawara, ko shawara, yana bayyanawa cêwa duk harshen da ya yaɗu sossai kamar Hausa, ba zai buƙace goyon baya da yawa daga wajen gwamnati da kuma Malamai kafin a karfafa shi a matsayin harshen tarayyar alʼumma."

Sun bayyana cêwa ana amfani da harshen Hausa a wurare da dama kaman Massallaci, iklisiya, wurin sanaʼa, da kuma sauran wuraren ayyuka kaman siyasa.

Rahoton ya ƙara bayyanawa cêwa harshen Hausa yana da fitarwa da amincewa a ƙasashen duniya. Sun ce wannan yana cikin manuniya cêwa ya kamata a soma aiwatar da Hausa a matsayin harshen tarayyar alʼumma.

ADVERTISEMENT

Bugu da ƙari, sun yi bayani cêwa an shaida muhimmacin harshen Hausa bayan manyan kamfanoni kaman Microsoft, Facebook, kafofin watsa labarai, Jamiʼun ƙasashen waje, da sauran wurare. Sun tabbatar cêwa idan aka ɗauki wannan shawara, Najeriya za ta samu ƙarin girma da cigaba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT