Labari daga Abuja tana mai tabbatar da cewa jamian rundunar farar hula ta DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin Nijeriya, sun hana maaikata da yan majalisa shiga.

Ana hasashen matakin shiri ne na daukar matakin tsige Bukola Saraki daga mukamin shugaban majalisar dattawa.

Majiyan mu a zauren majalisar sun ruwaito cewa ma'aikata da yan majalisar basu samu damar shiga zauren majalisar inda jami'an suka hana shiga ko fita tare da tare hanyoyi.

[No available link text]

An ji dan mjalisar, Sanata Abu Ibrahim yana cewa "Shin ko sojoji sun kwace mulki ne?" yayin da ya tarar da jami'an.

Wani kwakkwarar majiya ya shaida mana cewa jami'an sun tare zauren ne domin daukar matakin tsige shugaban majalisar wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ranar 31 ga watan Yuli.

Kawanya da jami'an suka yi ya biyo bayan ganawar da wasu sanatocin APC suka yi shugaban DSS tsakar daren ranar Litinin.

Majiya ya cigaba da cewa APC ya shirin kaddamar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar tare da Sanata Hope Uzodinma a matsayin mataimakin sa matukar idan an hana masu rike da matsayin daga shiga zauren yau.