Pulse.ng logo
Go

Tazarce Gwamnatin jihar Kano tayi maraba da wa'adin shugaban kasa

Sanarwar tace an samu karin masu tsaka jari a kasa bisa shirin tabbatar da adalci gwamnatin yanzu ta kafa

  • Published:
Full text of what Buhari said during Lake Chad conference play

Shugaba Muhammadu Buhari

(Presidency)

Gwamnatin jihar kano tayi maraba da wa'adin neman tsayawa takara da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Labarin haka yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishnan labarai da al'adu Mallam Muhammad Garba ya tura wa manema labarai a garin Abuja.

Sanarwa ta nuna cewa zarcewan shugaba zai taimaka wajen daura daga inda ta tsaya na shirin wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da harkar tsaro tare da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da adalci a ko wani fanni na gwamnati wanda ta fara shekara uku da hawa mulki.

Sanarwar tace an samu karin masu tsaka jari a kasa bisa shirin tabbatar da adalci gwamnatin yanzu ta kafa.

Hakalizalika matakin kawar da cin hanci da rashawa da yaki da ta'adanci ba tare da jinkiri da gwamnati keyi ya taimaka wajen gina martabar kasa a idon sauran kasashen duniya.

A ranar litinin neĀ  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da wa'adin tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa.

Lamarin ya tada kura a kasa inda har zuwa yanzu ana ta cece-kuce kan batun a kafafen sada zumunta.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.