Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya shigo sahun jiga-jigan jamiyar APC da suka sauya sheka daga jamiyar.
Gwamnan ya sanar da fitar sa daga jam'iyar wanda a karkashin ta yaci nasarar zama gwamna yau laraba 1 ga watan Agusta.
A gangamin sanar da matakin da ya dauka na barin APC da aka shirya a garin Sakkwato, gwamnan ya sanar cewa ya sauya sheka zuwa tsohon jam'iyar shi kuma babban jam'iyar adawa ta PDP.
Fitar sa ya daga adadin gwamnoni da suka bar jam'iya mai mulki zuwa uku. A baya gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom da na Kwara Abdulfatah Ahmed sun sanar da daukar matakin komawa PDP.
Tun ba yau ake harsashen fitar sa daga APC duba da irin tsokacin da yake yi game da yadda jam'iyar ke gudanar da alamuranta.
Matakin nasa ya biyo bayan Bolaji Abdullahi ya sanar da fitar sa ta kofar waje daga APC tare da ajiye mukamin kakakin ta.
Tsohon ministan wasanni ya bi sahun gogan sa a harkar siyasa kuma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya sanar da fitar sa daga APC ranar talata 31 ga watan Yuli.