Tauraron gasar kofin duniya, Brazil, ta sha kashi a hannun Belgium wasan su na zagaye na uku a gasar bana.

Fitattun yan wasan kasashen sun nuna gwaninta da dagiya sai dai daga karshe yan wasan kasar nahiyar turai suka samu galaba.

Belgium ta fara cin kwallo sakamakon barnar da Fernandinho yayi kana Kelvin De bruyne ya kara ma Belgium kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Cikin minti 71 bayan an dawo hutu sabon shiga, Renato Agusto ya cila kwallo a ragar Coutois da kai. Kwallon dai ya hazuka kokarin yan wasan Brazil inda suka yi iya bakin kokarin su wajen rama kwallaye  da Belgium ta ci.

Hakan bata samu ba har karshen wasan. Brazil wacce ta yi nasara daga kofin gasar duniya sau biyar tayi gida tare da takwaran ta na nahiyar kudancin Amurka, Uruguay, bayan ta sha kashi a hannun France a wasan su wanda aka tashi 2-0.

France da Belgium zasu kara a wasan daf da karshe na gasar ranar 10 ga wata.