ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dalilin da yasa gwamna ba zai iya yin takarar zaben 2019

A wasikar da gwamnan ya rubuta ma jam’iyar PDP, Fayose ya jaddada cewa fitowar shi takarar ban don ya kawo gaba ko kiyayya tsakanin yan jam’iyar, ya fito ne domin amfanin jam’iyar da yan ƙasa baki daya.

Wani jigon jam’iyar PDP Dr Okwesilieze Nwodo ya bayyana cewa gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ba zai samu damar fitowa takara karkashin jam'iyar a zaben 2019.

Ya bayyana haka ranar alhamis 28 ga watan Satumba a garin Abuja bayan sanarwan da gwamnan yayi ma jama’a cewa zai fito takarar shugaban ƙasa a zaben 2019 karkashin jam’iyar PDP.

Nwodo ya sanar ma kamfanin dillancin labarai (NAN) cewa bisa ga akidar jam’iyar gwamnan tare da sauran yan kudancin ƙasar baza su iya fitowa takarar shugaban ƙasa a zaben 2019.

Ya sanar cewa tun da aka kafa jam’iyar an riga an tsara yin takara a ko wani zabe zuwa yanki-yanki kuma a zaben 2019 yan takara zasu fito daga arewacin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Nwodo yana mai tabbatarwa cewa jam’iyar zata iya bakin kokarin ta wajen ganin cewa ko wani dan jam’iyar ya bi tsarin kundin tsarin dokar jam’iyar.

Yayi bayani cewa tun ba yau ba ake haka kuma wadanda suka nemi su fito takara alhalin ba yan yankin da doka ta amince da fitowar su basu ci nasara ba.

A wasikar da gwamnan ya rubuta ma jam’iyar PDP, Fayose ya jaddada cewa fitowar shi takarar ban don ya kawo gaba ko ƙiyayya ga yan jam’iyar, ya fito ne domin amfanin jam’iya da yan kasa baki daya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT