ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Falalu Dorayi ya fadakar a kan madigo da luwadi

Maudu'in sakon sa na wannan makon na daga cikin mummunar abun aibi dake neman yin kamari a cikin al'umma.

Kamar yadda ya saba a ko wani ranar Juma'a, jarumin ya tunatar da yan uwan musulmai kan daya daga cikin annobar da ya fado ga al'umma.

Babban jigon masana'antar fim yayi jawabi kan Luwadi da Madigo tare da bada nassi daga al-kurani da hadisi da kuma hanyar neman gafarar Allah.

Ga sakon da ya isar kamar haka;

ADVERTISEMENT

"M A D I G O  D A  L U W A D IMadigo da Luwadi masifu ne da suka ratsa tsakanin Al'umma Kauyuka da birane cikin duniya. Ma suyi maza da mata sun ajjiye tsoron Allah, sun biyewa shaidan domin sabawa Ubangiji da mafi muni da Kazantar sabo, wanda dabbobi ma basawa Allah hakan.Munin luwadi yasa Allah yai mummunar azaba akan mutanen Annabi LUUT, wadda kafin su baiwa wata Al'ummar irinta ba. Mala’iku ne suka ciccibe garin sukai sama dashi akai musu ruwan azaba da duwatsu na wuta aka Kifar dasu.Ubangiji (SWT) Yace; aNamli ayah ta 58“SAI MUKAYI RUWAN (DUWATSUN AZABA) AKANSU, LALLAI RUWAN DUWATSUN AZABAR NAN TA WADANDA AKAYI MUSU GARGADI YAYI MUNI KWARAI”Annabi (SAW) Yace;“Mafi girman abin da nake tsoracewa Al'ummah ta shine Irin aikin mutanen ANNABI LUUT”. Annabi (SAW) Ya kara cewa;“Tsinanane ne duk wanda yayi Jima'i da Dabba. Tsinanane ne duk wanda ya aikata irin aikin mutanen ANNABI LUUT.Madigo da Luwadi suna gadar da bala'i da masifu ga duk mai yinsu. Wallhi da ayi luwadi ko madigo da kai/ke gara ka/ki mutu, saboda girma da munin laifin a wajan Allah.Ku nemi gafarar AllahUbangiji (SWT) Yace; “Kace musu ya ku bayina wadanda Suka yima Kansu ‘Barna!! Karku fidda tsammani daga rahmar Allah. Hakika Allah yana gafarta dukkan zunubai baki daya, Shi shine Mai gafara kuma Mai Jin Kai"

ya kammala sakon da yin adduar "Allah ya shiryar damu yai mana rahma.Juma@tMbrk #sisters#brothers

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT