ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mai garkuwa da mutum wanda aka cafke ya kai karar babban sufeton na yan sanda

lauyan Evans ya kai karar ga kotu ranar laraba 28 na watan Yuni 2017.

Evans paraded with arms

Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ya kai karar babban sufeto na yan sanda Ibrahim Idris ga kotu bisa ga zargi tauya hakkokin shi.

Daily post sun rubuta cewa, Evans ya kai karar a babban kotun tarayya dake Lagos, inda yake neman kotu da ta tilasta ma hukumar yan sanda ta tuhume shi zuwa kotu ko ta sake shi.

Rahoto ya nuna cewa kakakin hukumar yan sanda na Lagos ASP Olarinde Famous-cole bai da wata masaniya game da karar.

Famous-cole yace, “Evans ya kai karar mu? Ban da labari akan batun, amma indai haka ne toh lalle bamu yi aikin da ya kamata.’’

ADVERTISEMENT

“Ku dawo gareni anjima, zan baku amsa indai muka samu tsammaci daga kotu”

Bisa ga labarin jaridar Vanguard, lauyan shi  Olukoya Ogungbeje ya kai karar ga kotu, inda yace hukumar yan sanda sun tauya hakkin shi.

Akalla anyi kwana 14 da tawagar Abba Kyari su ka kama wannan madugun yan garkuwa da mutum

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT