ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Babu abun da zai hana mu sallamar malamai 22,000

Gwamnan yace abun kunya ne a gan malamai sun gaza bada amshoshin jarabawan yaran firamari 4

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai yayi ikirari cewa barazanar kungiyar yan kwadago baza ta hana gwamnatin sa sallamar malamai 22,000 da suka gaza cin jarabawan da aka gudanar masu.

El-rufai yace gwamnati zata samu malamai 25,000 mafi cancanta wadanda zasu maye gurbin su.

Gwamnan ya sanar da haka a wata hira da musamman da yayi da wata gidan rediyo a garin Kaduna.

Yace ya kamata duk wani mai kishin jihar ya kunyata da gazawan malamai gurin bada amsoshi ga jarabawan yaran aji hudu na Firamare.

ADVERTISEMENT

Wannan martani ga barazanar da kungiyar malamai na jihar tayi na cewa zasu tafi yajin aikin idan gwamnati ta kuskura ta kori malaman.

Gwamnan yayi la'akari cewa lalacewar fannin karatu a jihar ya yawaita sanadiyar alfarmar da wasu yan siyasa ke baiwa malamai wadanda basu cancanta ba.

El-rufai yace majasar sa ta amince da baiwa malamai 25,000 aiki kuma hukumar SUPEB zata horar dasu kafin su fara koyarwa.

Daga karshe gwamnan yace duk wanda bai cancanta ba zai shiga aji domin koyarwa kuma gwamnatin Kaduna zata cigaba da yin bincike akan malamai domin tabbatar da managarta.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT