Pulse.ng logo
Go

Jarumin maza! Magidanci yayi fito-na-fito da barayi da suka nemi suyi masa sata duk da raunin harbin bindiga da ya samu

Daya daga cikin barayin da ake zargi yace basu yi niyar harbe harbe magidanci hakan ya faru ne bisa kuskure.

  • Published:
Meet Imo boys who camp at potholes to rob travelers at night play

Daya daga cikin barayin yace basu yi niyar harbe magidancin ba, hakan ya faru ne bisa kuskure

(PM NEWS)

An samu labarin jarumin magidanci da yayo kokawa da barayin da suka far ma gidan sa a jihar NIger duk da raunin harbin bindiga da ya samu.

A labarin da jaridar Punch ta fitar, rundunra yan sandan jihar sun kama barayin, Isah Kabiru da Abdullahi Musa bayan arangamar da ya faru a gidan Gado Aliyu.

Daya daga cikin barayin da ake zargi yace basu yi niyar harbe harbe magidanci hakan ya faru ne bisa kuskure.

Wakilin rundunar yan sanda, Muhammed Abubakar, yace ana daf da gurfanar da barayin gaban kotu domin fuskantar hukuncin doka kan laifin da ake zargi sun aikata.

Kamar yadda wakilin ya bayyana ma Northern City News, daya daga cikin barayin mai suna Sanda Chumo, ya tsare yayin da jami'an tsaro suka yunkura wajen kama su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement