Tsohon kakakin shugaban kasa marigayi janar Sani Abacha ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.
Tsohon sakataren watsa labarai na marigayi Abacha ya rasu a garin Jos
Ya rasu a safiyar talata 4 ga watan Yuli a wata asibiti mai zaman kanshi dake Jos, jihar filato
Jaridar premium times ta ruwaito cewa dansa Emmanuel Attah ya sanar cewa ya rasu a wani asibiti mai zaman kanshi a garin Jos a jihar filato ranar talata 4 ga watan Yuli 2017.
Tsohon ƙwamishnan labarai na jihar Benue ya sha fama da rashin lafiya kafin rasuwar sa.
Kafin kasancewar shi kakakin Abacha, Attah wanda ya kammala karatun sa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ya rike mukamin manaja mai kula da harkoki a ma’aikatar buga takardu na Benue Plateau Publishing Corporation (wanda ake kiran Nigerian Standard ayanzu).
Kuma yana cikin jagororin jaridar Daily Times dake legas.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng