ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Al-ameen Buhari

Ga wasu abubuwa biyar da muka fitar maku da baku sani ba game da wannan fitaccen jarumin.

___8905197___2018___9___26___17___buharialameen_37204843_2156291497947893_134933913796608000_n

Ya fiye fitowa a matsayin mugu ko mai muzgunawa kuma mafi yawanci fina-finan da yake fitowa a matsayin jarumi tana fadakarwa sosai.

Ga wasu abubuwa biyar da muka fitar maku da baku sani ba game da wannan fitaccen jarumin kamar haka:

1. Shi haifafen dan garin Jos ne  amma yayi karatun addini almajiranci a jihar Nasarawa. Sanda yake karatu ya kan yi wa'azi a masallatai.

ADVERTISEMENT

2. Bayan kallon shirin fim da Ali Nuhu da Fati Muhammed suka fito a matsayin jarumai ya yanke shawarar shiga masana'antar Kannywood.

A cewar shi bayan kallon shirin 'Nazari' wanda tsohon babban mai shirya fim, Yusuf Khalid, ya shirya ya dau matakin shiga harkar fim.

3. Yayi aikin direban mota gabanin fitowa a shiri

ADVERTISEMENT

Al-ameen Buhari yayi aikin direba mai safarar ma'aikata da jarumai  zuwa wuraren daukar saitin fim gabanin ya fara fitowa  a matsayin jarumi.

4. Fim na farko da ya fara fitowa a cikin ta shine "Fargaba" wanda Salisu Mu'azu ya shirya.

Yayi da kudin da ya samu na fitowa a shirin wajen ciyar da mara hali tare da yin barar addu'a gare su domin samun nasara da daukaka a sana'ar da ya zaba ta yin fim.

5. Cikin fina-finai da dama da yayi uku suka fi soyuwa a gare shi.

ADVERTISEMENT

Al-ameen Buhari ya fi son  shirin "Fari da baki" wanda Aminu Saira ya shirya da shirin "Ahlil Kitab" wanda Adam Zango ya shirya da kuma "Azal" wanda kamfanin 3SP ta dauki nauyin shirayata.

Ya zabi fina-finan ne bisa ga labarun da suka kunsa da kuma fadakarwar dake cikin su.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT