ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dakaru 8,000 aka baje a sassa daban daban na garin Kaduna domin hana kungiyar kwadago zanga-zanga

Ana sa ran cewa shugaban kungiyar NLC na kasa Ayuba Wabba zai jagoranci sauran mukarabben sa wajen gudanar da zanga-zangar adawa kan korar ma'akata da gwamnatin jihar tayi.

An tura dakarun yan sanda 8,000 zuwa sassa daban daban a garin Kaduna domin shawo kan yan kungiyar kwadago dake zanga-zangar adawa kan koran ma' aikata 36,000 da gwamna Nasir El-rufai yayi.

Kamfanin dilancin labarai ta NAN ta ruwaito cewa an tura jami' an zuwa wurare daban daban na jihar ciki har da babban ofishin kungiyar dake jihar.

Wannan yunkurin ya janyo karancin mutane da raguwar aika-aikar jama'a a garin. Akwai karancin motocin haya a tituna.

Ana sa ran cewa shugaban kungiyar NLC na kasa Ayuba Wabba zai jagoranci sauran mukarabben sa wajen gudanar da zanga-zangar adawa kan korar ma'akata da gwamnatin jihar tayi.

ADVERTISEMENT

Jami'in hulda da jama'a na jihar Muktar Aliyu ya sanar ma wakilin NAN cewa an tura dakaru 8,000 zuwa birnin Kaduna domin shawo kan zanga-zangar tare da tabbatar da zaman lafiya ga al'ummar jihar.

A wata sanarwa da aka fitar ranar laraba, gwamnatin jihar tare da hukumar yan sanda na jiha sun hana yin zanga-zanga na ko wani iri a fadin jihar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT