Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kori shugaban hukumar rundunar fararen hula ta DSS Lawal Daura daga aiki.

Wannan labari ya fito a cikin wata sanarwa da kakakin sa Laolu Akande ya fitar ranar talata 7 ga watan Agusta. Mai'akaci mai rike da mukami mafi girma a hukumar zai maye gurbin sa.

Sai dai sanarwar bata bayyana dalilin daukar wannan matakin da shugaba mai riko yayi ba, ana hasashe cewa korar ta biyo bayan lamarin da ya faru a zauren majalisar tarayya inda jami'an rundunar DSS suka mamaye zauren tare da hana ma'aikata da yan majalisar shiga.