Yar majalisar wakilai dake wakiltan jihar Ribas Boma Goodhead tayi halin maza inda take fito-na-fito da jamian rundunar DSS ta suka tare hanyar shiga farfajiyar majalisar dokoki.

A cikin bidiyo da majiyan mu suka turo mana, an gan inda yar majalisar take daga murya ga jami'an da suka sirrace fuskokin su tana mai cewa "Sai ku bari ana amfani daku wajen cin mutunci, kuu kashe mu idan zaku iya, mutane nawa zaku iya kashewa a nan?".

[No available link text]

Jami'an sunyi ma zauren majalisar kawanya ne a safiyar yau inda suka hana ma'aikata da yan majalisar shiga harabar zauren.

Wani kwakkwarar majiya ya shaida mana cewa jami'an sun tare zauren ne duk cikin matakin tsige shugaban majalisar wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ranar 31 ga watan Yuli.

Kawanya da jami'an suka yi ya biyo bayan ganawar da wasu sanatocin APC suka yi shugaban DSS tsakar daren ranar Litinin.

Majiya ya cigaba da cewa APC ya shirin kaddamar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar tare da Sanata Hope Uzodinma a matsayin mataimakin sa matukar idan an hana masu rike da matsayin daga shiga zauren yau.