Kotin koli dake Abuja ta wanke karar zargin da aka shigar ma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, a zaman da alkalai biyar wanda Justice Dattijo Muhammad ya zama jagora suka gudanar kan karar ranar juma'a 6 ga watan Yuli, alkalan sun kawar da zargin da ake ma Bukola Saraki.

Hakan ya faru ne bayan da suka kalubalanci  karar da aka shigar kan rashin tabbataciyar hujja game da zargin.

A zaman da aka yi ranar juma'a, alakalan sunce hujjar da aka kaddamar gaban kotu bata kai ga zama abun lura ba saboda jita-jita ne wanda bai da tushe.

Justice Centus Nweze ya karanta hukuncin da aka zartar kan karar bayan alkalan sun kawar da hujjar da aka bayyana kan zargin.

Hukuncin  ya kalubalanci matakin da kotun daukaka kara ta dauka kan karar inda masu shari'ar suka ce matakin bai kai ga hakan ba.