Jami'an tsaron sun tare hanyar shiga gidan shi dake nan unguwar Lake Chad na Maitama dake nan Abuja safiyar ranar talata 24 ga wata. Wanna ya biyo bayan tsammacin da sufeton yan sanda ya tura ma shugaban majalisar da ya bayyanar da kan sa ofishin yan sanda domin bada amsar zargin da ake masa na goyon bayan yan fashi da makami da suka kai hari garin Offa.
Sai dai matakin bata cinma manufar ta ba. Bayan tare hanya da jami'an suka yi a tun safiyar asuba na ranar domin bayan nasarar da shugaban majalisar yayi na tserewa sanatoci 15 suka sauya sheka daga jam'iya mai mulki na APC zuwa PDP da ADC.
Yadda ya kaurace daga kamuwa
Wani shaidar gani da ido ya shaida mana cewa Bukola Saraki ya tsere daga gidansa ta hanyar wata karamar kofa kana ya garzaya zauren majalisar tarayya cikin tasi.
Wani ma'aikacin majalisar ya tabbatar da hakan inda ya bayyana mamakin sa ganin motar da jagoran yan Nijeriya na uku ya fito daga ciki.
A jawabin sa a zaman majalisar da ya jagoranta Saraki yace da taimakon Allah ya tsere daga kamuwa.
Yace yan sandan sun tare hanyar shiga ko fita daga layin gidansa tun karfe 6:30 na safe.
Yana mai cewa "Sun hana tawagar motoci na fita. Kasancewa nima na shirya ma wannan ranar, na ajiye wata mota wanda zata fitar dani."
Ya kara da cewa mataimakin sa Ike Ekweremmadu ya kira shi domin sanar mashi cewa ba zai samu damar zuwa majalisar ba.
Mun samu labari cewa jami'an rundunar DSS da na hukumar EFCC sun mamaye gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, dake nan unguwar Apo tun da asuba.