ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Maganar Buhari ga gwamnoni akan rashin biyan albashin ma'aikatan jihohin su

Buhari yace yana mamakin yadda gwamnonin ke iya bacci alhali sun ki biyan ma'aikata albashi

Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari yayi Allah -wadai da halin da gwamnoni ke nunawa alhali sun ki biyan ma'aikatan jihohin su albashin su.

Shugaban yayi korafi akan batun ranar talata 17 ga watan Octoba yayin da ya amshi ziyarar gwamnoni a fadar sa inda yake cewa dole su biya ma'aikatan cikiin gaggawa domin wasu daga cikin su basu iya biyan bukatun su.

"ta yaya mutum zai iya bacci cikin nashuwa alhali bai biya ma'aikatan shi albashin watanni da dama" yace.

"A kullum ina ta tunani yanda ma'aikata ke ciyar da iyalen su, yadda suke biyan kudin hayar gidajen su har ma da yadda suke biyan kudin makarantar yaran su".

ADVERTISEMENT

Shugaban ya kalubalenci yaɗuwar rashin biyan albashin a jihohi daga misani ya kara da cewa ya zama dole gwamnatin tarayya da na jihohi su hada kai wajen tabbatar da cewa ko wani ma'aikaci ya samu abun da yake bukata a duk fadin ƙasar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT