Fadar shugaban ƙasa ta zabi wasu gwamnoni 6 da zasu ziyarci shugaban ƙasa a birnin London inda yake jinya cikin har da gwamnonin jam’iyar adawa na PDP.
Gwamnonin PDP zasu ziyarci shugaban ƙasa
An zabi gwamnonin da zasu ziyarci shugaban daga fadar shugaban kasa
A bisa ga labarin jaridar Punch gwamnonin zasu bar ƙasa yau talata 25 ga watan Yuli.
An zabi gwamnonin daga yankuna shida na kasar.
Babu ingantaccen labarin ko mai ba shugaban kasa shawara a kan harkan tsaro manjo janar Babagana Munguno ya zabi gwamnonin ƙasancewa shi ya shirya tafiyar.
Wasu daga cikin gwamnonin da zasu yi tafiyar akwai Udom Emmanuel na jihar Akwai ibom, Dave Umahi na Ebonyi, Abdul’aziz Yari na Zamfara da Abiola Ajimobi na jihar Oyo.
Punch ta ruwaito cewa wani gwamna wanda baya cikin tawagar ya bayyana cewa an zabi gwamnonin daga fadar shugaban ƙasa ba daga majalisar gwamnoni na ƙasa.
Wannan tafiyar zai faru kwana biyu bayan ziyarar da wasu gwamnoni da jigajigan jam’iyar APC suka kai ma shugaban a inda yake jinyar rashin lafiya.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng