ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

wani jigon ƙungiyar yan ta'adda da abokan sa guda 3 sunyi da na sani sun miƙa wuya

yan ta’addan sun miƙa wuya ga rundunar sojoji na bataliya 120 task force a garin goniri dake jihar Borno

Boko Haram's shadowy leader, Abubakar Shekau

Kasurgumi dan ƙungiyar boko haram tare da wasu abokan sa sun tuba kuma sun miƙa wuya ga rundunar sojoji ranar litinin.

Jami’in hulda da jama’a na sojoji janar Sani Usman ya sanar da haka a garin Abuja ranar talata 18 ga watan Yuli.

Usman yace cikin wadanda suka mika wuya akwai wani ameer na ƙungiyar boko haram mai suna Konto Fanami.

Kakakin rundunar sojoji yace musamman yan ƙungiyar suka miƙa wuya ga rundunar sojoji na bataliya 120 task force dake garin Goniri a jihar Borno.

ADVERTISEMENT

Yayi kira ga sauran yan ƙungiyar dake da niyar barin ƙungiyar da su bi sahun Fanami da abokan shi.

Ya kara da cewa a shirye rundunar sojoji suke wajen tarban wadanda ke da niyar miƙa wuya kuma za’a amshe su cikin hannu biyu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT