ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

korarren jami’in sojojin sama yana cikin yan ta’adda da yan sanda suka kama a jihar Kano

wasu yan ƙungiyar boko haram sun duƙufa da yan sanda wajen harbe-harbe a safiyar ranar lahadi

an kama yan ta'addan tare da makamai da dama

Wani korarren jami’in rundunar sojojin sama yana cikin yan ta’adda da rundanar yan sanda na jihar Kano suka kama

Bisa ga rahoto da aka fitar, wasu yan ƙungiyar yan ta’addar sun duƙufa da da yan sanda wajen harbe-harbe a safiyar ranar lahadi 23 a watan Yuli.

Yan sanda sun ci nasarar kama wasu guda 5 cikin yan ta’addan a yankin Gayawa na karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano.

ƙwamishnan yan sanda na jihar Rabiu Yusuf ya sanar cewa an kama mutum biyar din ta hanyar fasaha da runduanar yan sanda ta amfani da ita don kama wasu yan kanzagi da suka gudu daga dajin sambisa domin su tattaru a wasu jihohi don cigaba da manufar su.

ADVERTISEMENT

Rabiu ya kara da cewa don tabbatar cewa basu yada manufar su shi ne yasa babban sifeton yan sanda ya kafa wasu runduna ta musamman karkashin jagoran kwamishna yan sanda na jihar Kano don farautar yan ƙungiyar da suke neman tattaruwa a yankunan jihar.

A yayin da wasu daga cikin yan ƙungiyar ke neman kai farmaki wasu yan ƙungiyar boko haram 9 sun mika wuya ga rundunar sojoji a ranar asabar 22 ga watan Yuli a yankin Buni yari na karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT