ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dakarun sojoji sun ƙashe yan ta’adda biyar a jihar Borno

An harbi yan darikar boko haram yayin da suke neman yin satar kayan abinci a wani ƙauye

A Nigerian soldier patrols in the town of Banki in northeastern Nigeria on April 26, 2017. Banki has been totally destroyed during battles between the Nigerian army and Boko Haram insurgents. Over 32,000 people live in the town but free movement is limited.

Dakarun sojoji dake yaki da yan boko haram sun ƙashe wasu da ake zargin cewa yan darikar boko haram ne a ƙauyen mussini na jihar Borno.

An harbi yan ta’addar yayin da suke neman satar kayan abinci daga kauyen

Shafin Daily sun ruwaito cewa, bataliya 3 na birged 22 suka yi kwantan bauna harbin su yayin da aka sanar da zuwan yan ta’adda

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojoji brig.gen Sani Usman a bayanin shi yace,” mun gano wasu makamai daga yan ta’addar, aciki akwai bindigar  AK 47, mujallar AK 47, harsassai, kekuna 27, adduna 10 da wuka daya.”

ADVERTISEMENT

Wannan ya faru bayan wasu mata yan ƙonar bakin wake suka tada kansu da bam yayin da wasu yan banga suka gano su a wani gari mararrabar jihar da  kamaru.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT