Pulse.ng logo
Go

Bisa ga rahoton da ya fitar An sallami wakilin gidan rediyo na Freedom fm daga jerin yan jaridar gidan gwamnatin jihar Kano

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja

  • Published:
Wakilin freedom fm da aka sallama play

Wakilin freedom fm da aka sallama

Gwamnatin jihar Kano ta sallami wakilin gidan rediyon Freedom fm Abbass Yusha’u daga cikin yan jarida dake kawo rahoton gidan gwamnati.

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja.

A baya dai wakili daga ofishin yada labarai na gwamnatin ya tabbatar da labarin amma daga baya gwamnatin ta musanta haka.

Bayan aikawan da tayi ga gidan rediyon freedom fm na janye Abbas gwamnatin ta samu wani da zai maye gurbin sa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.