ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wata Balaraba a ƙasar Kuwait ta yi fushi bayan mijinta ya ƙara yin aure

Ga hotunan abinda ya faru bayan wata Balaraba ta samu labari cêwa mijinta ya auri sabuwar amarya.

 

ƘasarKuwaiti ƙasa ne mai arziki na man fetur da iskar Gas. Kusan duk wanda yake ɗan ƙasar Kuwaiti yana addinin musulunci. Saboda haka, namiji yana da damar auren mata har huɗu. Yawancin matan Kuwaiti basu son kishi. Suna son su zauna tare da mazajensu da kuma yaransu kawai.

A cikin waɗanan hotuna, wata ƴar kuwaiti ta yi babban ɓana bayan ta samu labarin kishiyan da aka yi mata. Wani mai suna Ali ya yi rahoto akan shafinsa na Tuwita cêwa wannan mata ta shiga da mota a guje cikin gidansu. Daga duk alamar, matan ta ɗauki wannan mataki saboda tsangwaman da take ji game da sabon auren da aka yi. Mota da gida, duk sun lallace sossai bayan ta rushe gina, kofa, tebur da sauran kayayyakin ɗaki.

A cikin rahotonsa, Ali ya cê matan ta yi bayani cêwa ta shigo da mota kai tsaye har cikin ɗaki domin taya ma maigidanta da sabon Amarya murna ga sabon rayuwa. Makwabta da ƴan uwa, sun yi haɗuwa a gidan domin bincika abinda ya faru. Har lokacin da muka karɓi rahoto, bamu sani ba idan akwai wanda ya ji rauni ko hasarar rai cikin wannan hatsari.

Mutane da dama suka yi tambaya: wani irin gaisuwa ne wannan? Mutane sun maida martani game da wannan matakin da ta ɗauka, amma wasu sun ce ta yi daidai.  Wani ya cê ya waye wannan mata da fitina tun ranar da aka yi auren ta.

ADVERTISEMENT

Menene raʼayoyinku ga matakin wannan mata?

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT