Tsohon shugaban kasa, cif Olusegun Obasanjo, ya karbi bakoncin Atiku Abubakar da wasu jagororin jamiyarb PDP a gidan sa dake garin Abeokuta nan jihar Ogun.

Ziyarar tasa tana dauke da mamaki duba da rashin jituwa dake tsakannin sa da tsohon jagoran Nijeriya wanda a karkashin shugabancin sa ya rike mukamin mataimaki.

Kwana biyu bayan samun nasarar Atiku, Obasanjo ya sanar cewa Allah ba zai yi masa gafara idan ya mara ma Atiku baya a zaben 2019.

Hirar shi da jaridar Premium times, Obasanjo ya sanar cewa kada Atiku yayi tunani cewa zai bashi goyon bayan sa domin cinma burin sa na zama shugaban kasar Nijeriya.

Sai dai tsohon jigon Nijeriya ya tabbatar da cewa babu wata gaba dake tsakanin su kawai dai sun samu tsabani ne a fanin siyasa.

Kamar yadda ya  sanar har yanzu shi da Atiku na da kyakkywar alaka a bangare lamuran walwala da sada zumunci.

Maganar tasa inda yake nuna cewa ba zai goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya jawo cece-kuce. Wasu na ganin cewa zaai koma goyon bayan dan takarar PDP.

Duk da cewa kai ga yanzu babu wani labari game da dalilin da yasa Atiku ya ziyarci Obasanjo, hotuna da suka fito sun nuna cewa ya tafi ne tare da shugaban jam'iyar PDP da kuma wasu jigan-jigan jam'iyar.