Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jamiyar PDP Atiku Abubakar yace Sule Lamido zai janye takarar sa domin shi.

Yayin da ya gana da magoya bayan PDP a garin Dutse nan jihar Jigawa ranar Litinin 10 ga watan Satumba, Atiku ya sanar cewa abokin takarar sa Lamido zai janye takarar sa domin shi saboda dan uwan sa ne kuma suna da ra'ayin mai kama a harkar siyasa.

Ya bada hujjar fadin haka bisa ga kisan tsohon shugaban kasa da dan uwan sa yayin da suka nemi fitowa takara a karkashin jam'iyar Social democratic Party shekarun baya.

A labarin da ya bada, Shehu Musa Yar'adua ya fito takarar kujerar shugaban kasa yayin da kanin sa Umaru Musa Yar'adua ya fito takarar gwamnan jihar Katsina. Sai dai daga baya kanin ya dakatar takarar sa domin baiwa yayan shi damar cigaba da manufar don samun nasara a zaben.

A cewar shi kwatankwacin haka zai faru domin Sule Lamido kanin sa ne.

Ya sanar ma jama'ar dake wajen taron da aka shirya musamman domin yakin neman zaben sa cewa mahaifiyar sa asali yar garin Jigawar sarki dake nan garin Dutse ce, a cewar sa daga baya ne iyalen ta suka yi kaura zuwa jihar Adamawa inda a nan aka haife.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kuma gana da abokin takarar sa Sule Lamido a asirce a gidan sa dake nan Bamaina na karamar hukumar Birnin Kudu.