Pulse.ng logo
Go

A garin Kaduna Yan sarasuka 50 da suka addabi al'umma sun shiga hannu

Jami'an tsaro sun kama su ne a sassa daban-daban dake fadin garin sakamakon binciken da suke game da tarzomar da wasu bata gari suka tayar kwanan baya.

  • Published:
Commission dismisses alleged filling of Jigawa quota with non-indigenes play Jami' an tsaro sun kama yan sarasuka 50 a garin Kaduna (Daily Post Nigeria)

Rundunar yan sanda na jihar Kaduna sunyi nasarar kama wasu yan sarasuka 50 da suka addabi al'umma.

Jami'an sun kama su ne a sassa daban-daban dake fadin garin sakamakon binciken da suke game da tarzomar da wasu bata gari suka tayar kwanan baya.

A wata sanarwa da ya fita, hadimin gwamnan jihar, mista Samuel Aruwan ya jinjina ma jami'an kana ya sanar cewa da zaran an kammala bincike za'a gurfanar dasu gaban kotu.

Ya bayyana cewa gwaman Nasir El-rufai ya samu labarin kamun da jami'an tsaron suka yi kuma yana mai kira na a tabbatar da shari'a bisa ga laifin da suka aikata.

Tun ba yau ba al'ummar garin Kaduna ke fuskantar barazanar yan sarasuka ko yan shara sai dai aika-aikan da suka yi kwanan nan ya jawo hankali wanda daga bisani gwamnan ya ziyarci al'ummar da lamarin ya faru.

Bayan ziyaran da ya kai ya umarci jami'an tsaro da suyi bincike cikin gaggawa domin kawo karshen aikin su.

 

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.