Shugaban ƙwamitin bada agaji na ƙasa Alhaji Aliko Dangote yace sun fitar da naira miliyan N250 don taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Benue.

Dangote a fadi haka a jihar Legas ranar lahadi bayan gwamnatin jihar Benue ta bukaci sanin taimakon da ƙwamitin ta bada.

A ranar 11 na watan Octoba 2012 ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa ƙwamitin mai mutane 34 wanda Dangote ke jagoranta don tallafawa wadanda riƙici ya shafa.

An kafa ƙwamitin don su taimakawa gwamnatin wajen bada agaji ma wadanda annoba ya fada masu a inda karfin gwamnati  bata kai.

Dangote ya kara da cewa kwamitin zata gina masauki ma wadanda ambaliyar ya raba su da gidajen su.

Shugaban ƙwamitin ya sanar cewa banda Benue kwamitin ta kara kai taimako ma wadanda ambaliya ya auka mawa a jihar Anambra da naira miliyan N150M.

Dangote yace ƙwamitin ta ba hukumar agaji na ƙasa (NEMA) naira miliyan N118M don ta kai kayan agaji ma jihohi da ambaliya ya ritsa dasu.