Bisa wannan kokari da tayi, jarumi wanda aka yi ma lakabi da Sarkin kannywood, Ali Nuhu ya yaba mata tare da wallafa hoton ta sanda take gudanar da rabon kayan masarufin a shafin sa na Instagram.

Tun ba yau ba, jarumar tana daya daga cikin fitattun masana'antar fim dake tallafawa mara sa galihu da arzikin da Allah ya azurta ta dashi.

Tana hakan ne a karkashin gidauniyar ta mai suna Hadiza Aliyu Gabon Foundation.

Hazikar jarumar tana daya daga cikin manyan jarumai da ake damawa dasu a masana'antar fim bisa rawar da take takawa a fim ta hanyar nuna kwarewar ta a ko wani matsayi da aka bata.