ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ma'aikatan tsaro sun kama masu garkuwa da mutane a jami'ar ABU

Shugaban ma'aikatan tsaro na jami'ar Jibril Tukur ya zanta wa manema labarai a ofishin sa cewa sun samu nasarar cafke masu laifin bayan bincike da bin diddigi kan aikin da suke

NAN ta ruwaito cewa masu laifin Halliru Sani mai shekaru 25 da Abdullahi Musa mai shekaru 30 yan asalin garin Samaru da Borno ne.

Shugaban ma'aikatan tsaro na jami'ar Jibril Tukur ya zanta wa manema labarai a ofishin sa cewa sun samu nasarar cafke masu laifin bayan bincike da bin diddigi kan aikin da suke.

Shugaban ya yaba jami'an hukumar bincike na jihar bisa gudummawar da suka bada wajen ganin cewa an samu nasarar garkame su.

Yace za'a gurfanar dasu ga yan sanda domin daukan matakin da ya kamata a hukunce.

ADVERTISEMENT

Yayin da suka zanta da yan jarida masu laifin sunyi nadamar aikin da suka tsinci kansu suna. Sun nemi gafara tare da yin alkawarin yin watsi da wannan mummunar aikin.

Tun ba yau ba al'ummar dake yankin jami'ar ke fuskantar barnar masu garkuwa da mutane tun ba ga dalibai ba kai ga malamai da sauran jama'a dake safara yankin inda makarantar yake.

A kwanakin baya an samu labarin wadanda suka yi awon gaba da uwargidan wani malami a jami'ar inda sai da aka biya tukuici kana aka sake ta.

Shi dai shugaban ma'aikatan tsaro ya sanar cewa shi da makaraban sa zasu iya bakin kokarin su wajen kawar da masu aiwatar da wannan mummunar barna a zauren makarantar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT