Jaruma mai tashe Rahama Sadau bata jinkiri wajen birge masoya da dinbim maabotan shafin ta da hotuna masu zafi.

Fitacciyar jarumar dake safarar kwarewar ta a harkar nishadi tsakanin masana'antar Kannywood da Nollywood ta saki wadannan hotunan a shafin ta na Instagram kuma masu bibiyan ta basu yi shuru wajen bayyana yadda ta birge.

Wannan ba shi bane karo da farko da jarumar zata dauki hankalin jama'a da hotunan ta.

Bana dai tauraruwar jarumar na haskawa a dandalin nishadi a gida da wajen ta. Ta fito a matsayin jaruma a fina-finai da dama na hausa da na turanci.

Ta kuma samu lambobin yabo bisa rawar da ta taka cikin fina-finan. Shirin wanda ta fara shiryawa mai taken "RARIYA" ya lashe kyautar gasar city people awards na 2017.

Tauraruwar ta kuma samu lambobin girmamawa daga jaridar Leadership tare da na wata kungiyar majalisar dinkin duniya.

Gidauniyar Global Women Empowerment network wanda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ta karrama ta da lambar yabo bisa rawar da take taka wa wajen daga tutar mata.