An samu labarin rasuwar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya kuma tsohon ministan kudi, Adamu Ciroma.

Kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito, marigayin ya rasu a wata asibitin kudi dake garin Abuja bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Tsohon jigon jam'iyar PDP ya rasu ranar alhamis 4 ga watan Yuli kuma yana yana da shekaru 84.

Haifafen dan garin Potiskum dake jihar Yobe, shine gwamnan babban banki tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.

Bayan haka ya rike matsaayin ministan kudi karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wa'adi na farko na mulkin sa.

Bugu da kari shine shugaban yakin neman zabe na Obasanjo yayin da tsohon shugaban ke neman zarcewa a zaben 2003.

Gabanin rasuwar sa, marigayin ya taka rawar gani a harkar siyasar kasar.