Jarumin fim kuma shahararen mawakin ya siya wa  mahaifiyar shi mota.

Ya wallafa bidiyon sanda ya mika motar ga mahaifiyar a shafin sa na Instagram tare da rubuta "Congratulation mum. ALLAH yasa ki kashe  ta...... Just bought a car for my mother!!.

A wani bidiyon da ya sake wallafawa a shafin nasa za'a gan inda yan uwan jarumin ke yi wa motar addua.

Abokan huldar sa da dimbin masoya masu bibiyan shafin nasa sun yaba masa bisa kokarin da yayi tare da yi masa fatan cigaba da kyautata wa mahaifiyar shi.

A kwannan nan dai da alama jagoran kamfanin White house family yayi karo da ni'imar Mahallici kuma baya boye ma jama'a falalar da ya samu. A cikin bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta kwanan baya anga inda yake tsokale jama'a da makudan kudi.

Hakan ya biyo bayan ya ziyarci fadar shugaban kasa domin yin bude baki tare da sauran abokan aikin sa na Kannywood da ketare.

Shugaba Buhari ya shirya liyafar bude bakidomin karrama wasu kungiyoyin matasa da shahararun mawaka da yan fim dake kasar ciki har da fitattun jaruman arewa.

Bugu da kari Adam Zango ya cigaba da nuna godiyan sa bayan fitar da kundin wakokin sa mai take "Mai laya" wanda za'a iya samu a kafafen yadda wakoki na zamani.