Mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Adam Abdullahi Zango wanda aka fi sani da A.Zango ya karyata zarge-zarge da ake masa na karban kudi domin yin wakar siyasa.

Zargin ya biyo bayan wani bidiyo da ya wallafa a shafin sa inda yake bin sabon wakar da yayi ma shugaba Buhari.

A wani sako da ya kara wallafa a shafin sa, Zango yace yana goyon bayan zarcewar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai domin sune zabin sa kuma zai cigaba da goyon bayan anniyar su gabanin zaben 2019.

Yana mai cewa "Bana siyasa don kudi.... Kuma babu wanda ya biyani nayiwa BABA buhari da mallam nasiru el'rufai waka!!.They are my choice & I will give them my support!!".

Ya kara da cewa kowa na da ra'ayin bin duk wanda yake so.

Mawakin ya fitar da wasu sabbin wakoki da ya rera na neman zarcewar shugaba Buhari.

Ga taken Wakokin kamar haka; 'Likitan Gyaran Nigeria' da 'Mu zabi Baba' da 'Tsintsiyace Alheri' sai kuma 'Kaduna sai mallam'.