ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sanata Misau ya ci zarafin sufeto janar na yan sanda a idon jama’a

Sanata Isah Misau ya bayyana wasu ayyukan barna da sufeton keyi yayin da ake zaman majalisa

Tun ba yau ba Dan majalisar dattawa Isah Misau da sufeton yan sanda Ibrahim Idris ke cikin halin kare -jini-biri-jini.

Gamawan su ya fara tun da dan majalisar ya zargi sufeton da yin almumdahana da naira biliyan 10 wanda ya kamata ya shiga asusun gwamnati.

Da haka kakakin hukumar yan sanda na kasa Moshood Jimoh yayi watsi da zargin.

Moshood ya kara da cewa sanatan ya gudu daga hukumar zuwa siyasa don amfanin kanshi kuma yayi karya da takardun sa.

ADVERTISEMENT

Ku sani cewa Sanata Isah Misau tsohon DSP ne na hukumar yan sanda kafin yayi murabus.

Tun bayan haka suke ta tsoki naman juna inda suke ta zargin juna da wasu miyagun laiffuka jefi-jefi.

Sai dai na wannan karon sanatan ya bayyana wani sabon zargi a idon jama’a yayin da suke zaman majalisa.

Ita dai zaman ana nunawa  kai tsaye a gidan talabijin na NTA.

Sanatan ya bayyana abubuwan dake ci masa tuwo tsakanin shi da sufeton yan sanda.

ADVERTISEMENT

Ga abubuwan da ya fada game da Sufeto janar Idris;

1. Yace kama Evans da yan sanda suka yi ba abun alfahari  bane

Kuna iya tuna wannan kasurgumin mai garkuwa da mutane Evans wanda yan sanda suka kama?

Misau yace hukumar yan sanda su daina murnar da kama shi da suka yi, domin kusan kowa na iya kama shi ba ma jami’ian hukuma kadai ba.

2. Yace Sufeton yan sanda yana soyayya da wasu jami’an hukumar guda 2

ADVERTISEMENT

Misau yana zargin sufeton da yin lalata da wasu jami’an hukumar yan sanda 2.

Dan majalisar yace sunansu Amina da DSP Esther.

3. Yayi ma daya daga cikin su ciki kuma ya aureta a asirce

A bisa bayanin Sanata Misau, Sufeto janar Idris yayi ma daya daga cikin matan da yake soyayya da su ciki kuma ya aureta 15 ga watan Satumba a asirce.

4. Yace Sufeto janar ya ƙarya dokokin hukumar yan sanda

ADVERTISEMENT

Misau yace sufeto janar ya ƙarya dokar hukumar yan sanda inda ya auri wata jami’in hukumar alhalin bata yi murabus ba kuma yin haka ya sabawa dokar hukumar.

5. Yace samun karin matsayi da sa mun matsayi a karkashin shugabancin Idris ana yin shi ne cikin rashin adalci

Dan majalisar yayi zargin Idris da baiwa “yaran sa” mukami a hukumar.

Majalisar dattawa ta kafa wata sabuwa kwamiti wanda zata binciki zargin da sanatan keyi ma sufeto janar na yan sanda.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT