Pulse.ng logo
Go

Taron maulidi na bana Abubuwan da ya faru a maulidin Sheikh Ibrahim Inyass

Taron wanda aka gudanar ranar juma'a da asabar ya samu halartar jama'a da dama daga kasashen Afrika daban daban mabiyan darikar tijjaniya

  • Published:
Dandazon jama'a daga kasashe daban daban na afrika sun halarci taron bikin maulidin Ibrahim Inyass play

Dandazon jama'a daga kasashe daban daban na afrika sun halarci taron bikin maulidin Ibrahim Inyass

(Twitter/aminugamawa)

Garin Abuja da Kaduna ta amshin dinbim jama'a a taro na 42 na daga bikin maulidin Sheikh Ibrahim Inyass wanda darikar Tijjaniya take shiryawa ko wace shekara.

Taron wanda aka gudanar ranar juma'a da asabar ya samu halartar jama'a da dama daga kasashen Afrika daban daban mabiyan darikar tijjaniya. Dandazon jama'a da suka halarci taron sun mayar da wajen taro na Eagles square da murtala square tamkar babu masakar tsinke.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron maulidi na bana play

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron maulidi na bana

 

Kamar yadda jagoran darikar tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sanar, makasudin taron shine don karrama babban malami Sheikh Ibrahim Inyass bisa gudummawar da ya bada na cigaban addinin musulunci a duniya.

Banda haka ga wasu muhimman abubuwa da ya faru a wajen taron:

Sheikh dahiru Bauchi ya kalubalanci yan darika kan katin Zabe

Jagoran darikar tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kalubalanci mabiyan akidar sa wajen samun katin zabe yayin da zaben 2019 ke gabatowa.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi play

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

(Daily Trust)

 

A bisa bayanin sa, babban malamin ya kalubalanci yan darikar tijjaniya da suyi gaggawa wajen mallakar katin zabe domin ita ce makami da zai taimaka wajen zaben shugabanni mafi soyuwa a garesu kuma wadanda zasu kawo sauyi da cigaba.

Ya kuma kira da ayi amfanin da katin wajen zaben shugabannin managarta masu kishin kasa kuma wadanda zasu biya bukatun jama'a da suke shugabanta.

Shugaban kasa yayi kira ga yan darika da suyi ma kasa addua

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Ibrahim Inyass ya taka muhimiyar rawa wajen  cigaban addinin musulunci a duniya.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi tare da ministan ilimi Malam Adamu Adamu play

Sheikh Dahiru Usman Bauchi tare da ministan ilimi Malam Adamu Adamu

Shugaban wanda ministan ilimi Adamu Adamu ya wakilta a wajen taron ya jaddada cewa gwamnatin tarayya zata cigaban da taimakawa tafiyar yan darika da yakinin samad da zaman lafiya a kasa.

Yayi kira ga jagorori da mabiyan darikar tijjaniya da su dukufa wajen yi ma kasa addua wajen samun cigaba.

Kwankwaso ya halarci wajen taron kuma ya samu karramawa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattawa mai zama, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana daga cikin manyan yan siyasa da suka halarci wajen taron.

Zuwan sa wajen taron, Sanatan ya samu karramawa daga cikin dinbim masoyan sa na daga cikin yan taron bikin.

 

Yan shi'a sun mara ma yan Darika baya

Wani abu da ya dauki hankali shine gudummawar da darikar yan shi'a wanda El-zakzaki ke jagoranta suka bayar ga yan tijjaniya don raya wannan ranar.

Kamar yadda muka samu labari sun bada gudummawar ruwan roba kwali-kwali ga yan taro tare da taya su murna zagayowar ranar haihuwar babban malami Sheikh Ibrahim Inyass.

Gudummawar yan shi'a play

Gudummawar yan shi'a

 

Iyalan Ibrahim Inyass sun nuna farin cikin su kan soyayyar da yan Nijeriya ke nuna ma mahaifin su

Iyalan Sheikh Ibrahim Inyass sun kasa boye farin cikin su bisa kauna da yan Nijeriya ke nuna ma mahaifin su.

A cewar su "Duk Duniya Babu Inda Ake Kaunar Mahaifinmu Kamar Nijeriya, Don Haka Muna Matukar Mika Godiyarmu Ga Tijjanawan Nijeriya".

Anyi rububi wajen hawan fitilar haska titi don sumbatar inda shehu ya bayyana

Abun fadi aji wanda ya kara daukar hankalin jama'a shine yadda wasu daga masu taro suka yi rububi wajen hawan fitalar haska titi domin sumbatar inda Shehu Ibrahim Inyass ya bayyana.

Mabiyan sunyi hakan ne bayan sun samu labari cewa shehin malamin ya bayyana a kololuwar fitilar a taron bikin wanda aka gudanar a garin Abuja.

 

Kamar yadda muka samu labarin taron bikin na bana wanda aka gudanar a Abuja yana daya daga cikin manyan taruka da aka gudanar a tarihin kasar.

Bayan taron da aka gudanar a Abuja an kuma hada wata a garin Kaduna wanda shima ya samu dandazon mabiya darikar tijjaniya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.