Rundunar yan sandan jihar Kebbi  sunyi nasarar kubutar da matar shahararren dan kasuwa mai dauke da juna biyu daga hannun masu garkuwa da mutane.

Hajiya Sadiya Tsoho, matar shugaban kamfanin Sha'aban supermarket ta fita daga shingen barayin ranar lahadi 8 ga watan Yuli.

Rundunar yan sanda ta jihar Kebbi ta sanar da haka inda tace hakan ya faru bayan sati daya da barayin suka awon gaba da ita.

Jami'in hukda da jama'a na rundunar, DSP Suleima Mustapha, ya sanar cewa jami'an rundunar sunyi nasarar kubutar da ita ba tare da biyan fansa ba.

Kamar yadda kakkakin ya bayyana uwargidan ta koma ga iyalen ta cikin koshin lafiya.

Yace yan sanda basu yi nasarar kama daya daga cikin barayin amma suna iyta bakin kokarin su wajen bin sahun barayin domin hutunta su.

Hajiya Sadiya ta hannun masu garkuwar ranar 1 ga watan Yuli bayan yan bindigar sun far ma gidanta dake nan Birnin-Kebbi.

Kamar yadda labari ya kawo mana barayin sun garzaya da ita sahara dake kauyen Mahuta na nan karamar hukumar Fakai ta jihar.