Gwamnan jihar Kano Alhaji Umar Abdullahi Ganduje wanda yake tsohon na hannun daman kwankwaso ne yayi watsi da jar hula.

Sanya jar hula alama ce ta nuna biyaya ga tsohon aminin shi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda suka raba gari bayan shekaru da dama da suka yi tare suna harkokin siyasa.

Hakan ya bayyana ne yayin da gwamnan ya karbi bakoncin tsohon gwamna Mallam Ibrahim Shekarau bayan komawar sa jam'iya mai mulki.

A cikin wata sako da ya wallafa a shafin sa na twitter, hadimin gwamnan Salihu Tanko Yakasai ya tabbatar da faruwar hakan inda ya rubuta cewa gwamnan yayi hanun riga da jar hula.

Hadimin ya kara da rubuta "Kano ta dinke! Aiki dai baba".

Mallam Shekarau ya kai ma gwamnan ziyara ne a ranar asabar 8 ga watan Satumba inda suka tattauna kan wasu batutuwa ta musamman.

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ziyarci Gwamna Ganduje sanye da bakaken tufafi, ya taras da Gwamna Ganduje sanye da nasa bakaken tufafin, ciki har da bakar hula - ba ja ba - kamar yadda ya saba.