Majalisar dokoki ta jihar Filato ta tsige kakakin ta, Peter Azi, bayan zaben kin jini da yayan majalisar suka yi.

Wannan matakin ya biyo bayan kudurin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Barkin Ladi yayi.

Yace majalisar ta dauki wannan matakin bayan da yan majalisa masu goyon bayan tsige shi sun samu rinjaye. Kamar yadda ya bayyana yan majalisar sun tsige shi ne bayan zaben kin jini da suka gudanar kuma masu goyon baya suka samu rinjaye.

Sakamakon matakin da suka dauka dan majalisa, Yusuf Gagdi, ya fitar da  Mista Joshua Madaki mai wakiltar kudancin Jos a matsayin wanda zai gaje shi.

Shima dan majalisar, Abdul Yanga ya amince da takarar Joshua a matsayin wanda zai maye gurbin wanda aka tsige wanda daga karshe majalisar ta tabbatar dashi a matsayi sabon kakakin ta.

A wani bangare kuma mutum 12 cikin 17 sun gudanar da zaben kin jini ga shugaban jam'iyar mafi rinjaye na majalisar. Yan jam'iyar na majalisar sun tsige Henry Yunkwap inda suka maye gurbin sa da Mista Na'anlong Daniel wanda ke wakiltar mazabar Mikkang na jihar.