Rundunar yan sanda dake nan jihar Adamawa ta tabbatr da cewa mutum 50 ne suka mutu sakamakon harin da yan kunar bakin wake suka kai a wata massallaci dake nan garin Mubi.
ADVERTISEMENT
Mutum 50 sun mutu sakamakon harin da yan kunar bakin wake suka kai a wata masallaci dake garin Mubi
Kakakin rundunar yan sanda na jihar SP Othman Abubakar ya tabbatar da haka ma manema labarai
Kakakin rundunar yan sanda na jihar SP Othman Abubakar ya tabbatar da haka ma manema labarai.
Yace wani matashi ne ya gabatar da harin yayin da musulmai ke sallar asuba.
Kamfanin dillancin labarai ta NAN ta ruwaito cewa harin ya faru ne a yankin Dazala dake karamar hukumar Mubi ranar talata a daidai karfe 5 na safe yayin da ake gabatar da sallar asuba.
ADVERTISEMENT
Lamarin dai shine na farko cikin shekaru uku tunda garin Mubi ta samu harin ta'addancin yan Boko Haram.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
ADVERTISEMENT
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng
ADVERTISEMENT