Wasu matasa dake goyon bayan zarcewar shugaba Muhammadu Buhari sun kwance zani a kasuwa inda suka kece ma juna raini yayin gudanar da taro a filin Eagle square.

Hayaniya ya faru a taron nuna goyon baya da kungiyar Buhari Youth Organisation ta shirya ranar Talata 10 ga watan Yuli a nan birnin tarayya.

Matasan sun shiga halin kokuwa yayin da aka fara rabon kayan kyauta a wajen taron. Anyi rige-rige wajen samun kyautar wanda bai kai yawan jama'ar da suka halarci taron.

Kamar yadda wakiliyar mu ta bayyana, wasu daga cikin matasan sunyi fito-na-fito da juna tare da amfani da sanda a matsayin makami.

Tarzomar da suka haifar bai sa an cigaba da manufar hada taron ba inda wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron suna masu gaggawa wajen barin filin taron tare da taimakon jami'an tsaro.

Hayaniyar ya cigaba da ci har tsawo sa'o'i biyu.

Kungiyar ta shirya taron ne domin nuna goyon baya da suke ma shugaba Buhari gabanin zaben nan gaba.

An gudanar da taron dai-dai lokacin da shugaban ya garzaya jihar Ekiti domin mara ma dan takarar kujerar gwamna baya gabanin zabe da za'a gudanar a jihar kwana-kwanan nan.