Advertisement

Hadiza Gabon ta birge cikin kayan anko da tayi da diyar ta

___8864617___2018___9___17___13___adizatou_41662342_688984621494232_5214956583686682631_n
___8864617___2018___9___17___13___adizatou_41662342_688984621494232_5214956583686682631_n
Idan baku sani ba jarumar Kannywood Hadiza Gabon tana da diya duk da cewa bata yi aure ba.
Advertisement

Fitacciyar Jarumar masanaantar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta birge tare da diyar Maryam a wannan hoton da suka yi.

Advertisement

Tauraruwar fim ta wallafa hoton su tare sanye da anko cike da fara'a a shafin ta na Instagram.

Idan akwai mai tunanin yadda rayuwa zata kasance idan mutum ya haihu, ganin yadda jarumar da diyar ta ke narkar da zukatan jama'a duba da irin wasa da dariya da suke yi zai taimaka wajen samun ansar farin cikin da haihuwa ke haddasa.

Ga masu neman sani, jarumar bata yi aure ba amma kuma tana da diya.

Hadiza Gabon ta karbi rainon Maryam Aliyu ne shekarun baya kuma tun lokacin shakuwar su na cigaba da kamari.

Advertisement

Ga masu bibiyan shafin ta na kafafen sadarwa, mawuyaci ne jarumar ta wallafa wani sako ko hoto a shafin ta ba tare da saka diyar ba.

Uwa da diya
Uwa da diya

Maryam ta zama tamkar jaruma ga wasu masu bibiyan shafin Hadiza, da yawa sukan bukace ta da ta isar da sakon gaisuwa ga diyar.

Hadiza Gabon tana son yin aure

Shahararriyar 'yar fim din Kannywood din nan, Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma lokaci ne kawai bai yi ba.

Advertisement

Da take hira da BBC, Hadiza ta ce aure lokaci ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi babu yadda mutum zai guje masa.

Hadiza Gabon, ta ce babu wacce za ta so ta rinka kaiwa-tana-komowa a gaban iyayenta ba tare da ta yi aure ba, alhalin kuma ta kai munzalin yin hakan.

"Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai lokacin aure amma ta ki yi" inji Gabon.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement