ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya taya jihar sa jimamin mutuwar babban limami

Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana

Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana.

A wata takardar sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya sa hannu, shugaban ya taya iyalan marigayi da sauran al'ummar jihar juyayin mutuwar sa.

Kamar yadda takardar ta bayyanar, Shugaban ya yaba halayen marigayin bisa yadda ya tafiyar da rayuwar sa wajen raya addinin musulunci.

yayi kira ga jama'a da a yi koyi da kyakkywar halin  sa na zama tare da mutane cikin soyayya da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa da makwabta da sauran jama'a.

ADVERTISEMENT

Daga shugaban, ya yi ma marigayin addu'ar Allah ya jikan shi da rahama tare da yi iyalen sa addu'ar Allah ya basu hakurin jure rashin sa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT