ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Har yanzu Yusuf na jinya a Nijeriya, bai tafi kasar waje

Kakakin shugabankasa yayi watsi da labari dake yaduwa cewa an tafi da Yusuf Buhari kasar waje domin jinya

Babban mai yi wa shugaban hidima a fannin watsa labarai Garba Shehu ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar alhamis 28 ga watan Disamba.

A bisa ga rahoton da jaridar The Cable ta fitar, ana zargin cewa an tafi da Yusuf kasar Jamus domin jinyar raunin da ya samu sanadiyar hatsarin babur da ya samu safiyar ranar alhamis.

Shi dai kakakin wanda shine ya sanar da labarin hatsarin ga jama'a yace har yanzu Yusuf na nan a wata asibitin kudi inda yake jinya kana ya kara da cewa labarin dake yaduwa na cewa an tafi dashi kasar waje labari ne mara tushe.

ADVERTISEMENT

A safiyar ranar laraba 27 ga wata Shehu ya sanar cewa Yusuf Buhari ya ji rauni tare da karaya sanadiyar hatsarin babur da ya samu a yankin Gwarinpa nan babban birnin tarayya daren ranar 26 ga watan yau.

SHi dai kakakin ya sanar cewa anyi Yusuf tiyata kuma yana murmurewa.

Daga karshe kakakin ya sanar cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika godiya ga yan kasar bisa addu'o'i da suke yi game samun lafiyar dan shi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT