ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

kwararriyar likita tayi kira na a haramta sayar da maganin tari

Tayi wannan kiran a wani taro kan batun amfani da miyagun kwayoyi wanda majalisar dattawa ta gabatar a jihar Kano

Tayi wannan kiran ranar litinin a garin Kano yayin da yan majalisar dattawa suka hada wani gaggarumin taro kan amfani da miyagun kwayoyi.

Tace Nijeriya na bukatar kwakwarar yaki da amfani da miyagun kwayoyi kuma tayi kira na a lura da yanayin yadda ake safarar magunguna a biranai da kananan hukumomi.

"Ya kamata jama'a da sarakunan gargajiya da cibiyoyin kula da masu tabin hankali su hada gwiwa wajen yakar yawan amfani da miyagun kwayoyi a jihohi da ma kasar baki daya"tace.

Shima wani jigo a hukumare NAFDAC Dr Umar Usman ya jaddada kan batun inda shima yayi kira ga jama'a da su taimaka wajen ganin an cinma burin yakar amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar.

ADVERTISEMENT

"Ya kamata a hukunta duk wani mai sayar da magunguna irein su Codein ga matasa  domin su zama abun lura ga sauran masu ire-iren sana'ar"yace.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT