Advertisement

Tsohon kwamishna yayi ma gwamna mai zama fata-fata a zaben Legas

Tsohon kwamishnan wanda yayi aiki da gwamnatin Bola Tinubu da Babatunde Fashola yayi ma gwamna Akinwunmi Ambode fata-fata domin zama dan takarar APC a zaben 2019.
Advertisement

Tsohon kwamishnan kasuwanci da masanaantu, Babajide Sanwo-olu yayi zarra a zaben fidda gwani da aka gudanar jihar Legas.

Advertisement

Tsohon kwamishnan wanda yayi aiki da gwamnatin Bola Tinubu da Babatunde Fashola yayi ma gwamna Akinwunmi Ambode fata-fata domin zama dan takarar APC a zaben 2019.

A sakamakon zaben da aka fitar, Sanwo-Olu ya baiwa Ambode tazarar kuri'u mai yawan gaske.

Shugaban jam'iyar APC na jihar Legas, Tunde Balogun, ya sanar da sakamakon zaben tare da kawar da labarin soke zaben da kwamitin uwar jam'iyar tayi.

A sanarwar da ya fitar, Sanwo- Olu ya dankari gwamna mai saman kujera da kuri'u mafi rinjaye.

Advertisement

Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u 970, 851 yayin da gwamna Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72, 901 cikin kuri'u sama da miliyan daya da aka kada.

Bisa ga wannan sakamakon shugaban ya kaddamar da Sanwo-Olu a matsayin wanda zai daga tutar APC a zaben 2019.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement