Advertisement

Shugaba Buhari ya taya Gboyega Oyetola murna

L-R: Governor Rauf Aregbesola, Gboyega Oyetola and President Muhammadu Buhari
L-R: Governor Rauf Aregbesola, Gboyega Oyetola and President Muhammadu Buhari
Shugaban yayi kira ga sauran yan takara da suka yi takarar zaben amma basu amince da sakamakon da su garzaya kotun daukaka kara don shigar da kara.
Advertisement

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya dan takarar APC, Gboyega Oyetola, murnar lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Advertisement

Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben bayan karashen zaben da aka sake yi ranar Alhamis 27 ga watan Satumba.

Dan takarar APC ya doke abokin takarar shi na PDP, Sanata Ademola Adeleke, da kuri'u 483.

Gboyega Oyetola
Gboyega Oyetola

A cilkin wata sanarwa da kakakin sa, Garba Shehu, ya fitar ranar Juma'a, shugaban ya taya Oyetola da jam'iyar APC murna na lashe zaben gwamnan Osun.

Advertisement

Shugaban yace nasarar da aka samu wajen gudanar da zaben ba tare da wata tarzoma na tabbatar da cewa tsarin dimokradiya na samu inganci a kasar. Yayi kuma jinjina ma hukumar INEC.

Shugaba Buhari ya kuma yi ma al'ummar jihar Osun godiya bisa damar da suka baiwa dan takarar APC na zama gwamnan su kana ya yaba ma gwamna mai ritaya, Rauf Aregbesola, bisa ayyukan da yayi a jihar.

Daga karshe shugaban yayi kira ga sauran yan takara da suka yi takarar zaben amma basu amince da sakamakon da su garzaya kotun daukaka kara don shigar da kara.

Yayin da yake jawabi bayan sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben, zababben sabon gwamnan ya mika godiyar sa ga shugaban bisa goyon baya da yayi mashi da kuma rawar da ya taka wajen tabbatar da ingantacciyar zabe.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement