Advertisement

Gwamnan Legas ya sha kashi, APC ta kaddamar da Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zabe

Jam'iyar ta kaddamar da sakamakon zaben duk da cewa kwamitin dake sa ido ga zaben jihar da uwar jam'iyar ta tura jihar ta soke zaben.
Advertisement

Gwamna Akinwunmi Ambode ya sha kashi yayin da jamiyar APC ta jihar Legas ta kaddamar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda da gwani da aka gudanar a jihar ranar Talata 2 ga watan Octoba.

Advertisement

Shugaban jam'iyar APC na jihar Legas, Tunde Balogun, ya sanar da sakamakon zaben tare da kawar da labarin soke zaben da kwamitin uwar jam'iyar tayi.

A sanarwar da ya fitar, Sanwo- Olu ya dankari gwamna mai saman kujera da kuri'u mafi rinjaye.

Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u 970, 851 yayin da gwamna Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72, 901 cikin kuri'u sama da miliyan daya da aka kada.

Bisa ga wannan sakamakon shugaban ya kaddamar da Sanwo-Olu a matsayin wanda zai daga tutar APC a zaben 2019.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement