Hukumar hana cin hanci da rashawa na EFCC reshen jihar Kaduna ta gurfanar da wani dattijo mai suna Hussaini Baba a gaban mai shari'a S.M Shuabu na babbar kotun tarayya dake Kaduna kan zargin amfani da kudin bogi.
Malam Hussaini Baba mai shekaru 65, wanda manomi ne kuma dan asalin karamar hukumar Jahun dake jihar Jigawa, hukumar kare lafiyar fafaren hula (NSCDC) ne suka mika shi ga EFCC bayan sun kama shi a lokacin da yake amare da kudaden bogin a garin Rigachikun.
An kama shi ne da kwayar takardar naira dari biyar guda 303 da kuma kwayar takardar naira dubu daya guda 32, wanda a jimlance kudin ya kai N183,500.
Bincike ya nuna cewa Malam Husseini ya jima yana wannan harka ta amfani da kudaden bogi har ma ya shaida cewa ya kan siyar da su a kan dubu sha biyar (N15,000) ga masu bukata a nan jihar Kaduna har da jihar Katsina.
Daga bisani dai, Malam Husseini ya musanta zargin da ake yi masa, inda alkali ya ki bada belinsa kasancewar babu lauyan da ya tsaya masa.
Alkalin ya bada umarnin a ci gaba da tsare dattijon har zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, 2017 da za a ci gaba da sauraren karar domin bada belinsa.