Advertisement

Gwamna yá dakatar da ʼƴan jarida biyu daga yin rahoto akan ayyukan Gwamnati

___5806162___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___5806162___2016___11___24___16___tanko-Al-Makura
___5806162___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___5806162___2016___11___24___16___tanko-Al-Makura
Al-makura bai ji daɗin yadda ʼƴan jarida biyu sun yi rahoto a kan wasu shuwagabanin ƙungiyar ƙwadago wanda aka kashe.
Advertisement

Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko A-Makura ya dakatar da ʼƴan jarida guda biyu daga yín rahoto a kan dúk abinda ya shafi ayyukán Gwamnatin Jihar Nasarawa.

Advertisement

An dakatar da Umar Muhammad na Gidan Jaridan Punch da Rabiu Omaku na Gidan Jaridan Universal Reporters wanda yake yanar gizo, daga yin rahoto a kan ayyukan Gwamnatin Jihar Nasarawa.

Muna da rahoto cewa akwai saɓani tsakanin Mashawarcin Gwamna akan harkokin watsa labarai- Ahmed Tukur da Muhammad.

'Ƴan jarida wanda gwamnati ta dakatar da su a jihar Nasarawa, sun zama biyar.

Shugaban masu rahoto na Jihar Nasarawa, Mr Suleiman Abubakar ya yi wannan sanarwa cewa Gwamnatin Nasarawa ta hana Muhammed da Omaku daga yin rahoto.

Advertisement

Abubakar ya ce:

“Mashawarcin Gwamna Al-Makura  a kan harkokin watsa labaru ya ce an dakatar da ku biyu (Muhammed da Omaku) har abada abadin, daga yin rahoto a kan ayukkan gidan gwamnati da ayyukan gwamnatin Nasarawa gaba ɗaya. Ya ce wannan umarni daga wurin maigidansa ne.”

Sauran ʼƴan jarida wanda aka dakatar da su daga yin rahoto game da ayyukan Gwamnatin Nasarawa su ne; Mary Amirikpa na Gidan Labarai na Jihar Nasarawa, Iliya Audu na Nigerian Newsday, da Sofia Ogaze na Television Continental.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement